Fitaccen dan wasan na Portugal yana son A Biya fam miliyan 5.5 Akan tsohon gidansa
Cristiano Ronaldo zai sayar da katafaren gidansa na alfarma bayan komawarsa Saudiyya a watan Disamba. Gidan Yana a unguwar Alderley Edge, jaridar The Sun ta bayar da rahoton cewa farashin da aka Kayyadewa gidan ya kai fam miliyan 5.5 (fiye da dala miliyan 6.5).
Wakilin gidaje Jackson-Stops (mai kula da siyar da kadarorin) ya bayyana wannan katafaren gidan a matsayin “babban Gida Kirar zamani”.
Gidan zama ne mai masaukin baki, wurin shakatawa na cikin gida, dakin motsa jiki na zamani, filin wasa da filin wasan tennis, wurin Ninkaya da shakatawa, da kuma katon dakin sinima.
Ronaldo dai ya bar Manchester United ne a cikin wani yanayi mai cike da rudani sakamakon komawarsa kungiyar da matsaloli da dama.
Bayan gasar cin kofin duniya, fitaccen dan wasan Portugal ya rattaba hannu a kungiyar Al Nassr, kungiya daga gasar Saudi Arabiya, na Kakar Wasa biyu da albashin kusan Yuro miliyan 200 a kowace kaka.
Daga Mujallar Marca .
Fassarar Saliadeen Sicey