Kotun Ƙoli ta tabbatar da Ademola Adeleke a matsayin cikakken zaɓaɓɓen gwamnan jihar Osun.
Kwamitin alkalai na mutum biyar, ƙarƙashin jagorancin John Okoro, ya tabbatar da hukuncin da Kotun Daukaka Ƙara, wanda ya tabbatar da Adeleke a matsayin gwamna.
Da yake jawabi bayan hukuncin kotun, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya Adeleke murna ne, sannan ya bukaci tsohon Gwamna Oyetola da ya je ya hada hannu da sabon gwamnan domin ciyar da jihar gaba.