Kano Ayau Hausa, Siyasa

Buhari ya bukaci gwamnoni su taimaka masa wajen zabo wanda zai gaje shi

Idan ba a manta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnoni da kuma shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu a fadar shugaban Kasa kafin ya tashi zuwa taro a kasar Spain ranar Talata.

A wurin wannan taro, Buhari ya gargaɗi gwamnoni da shugaban jam’iyyar da su tabbata an samu haɗin kai a cikin jam’iyyar domin a zaɓi ɗan takara mai nagarta da kishin talakawa wanda ko bayan ya ci zaɓe zai yi tasiri a zukatan ƴan ƙasa.

Bayan haka shugaba Buhari ya ce shi da kansa ya ke so ya zaɓi wanda zai gaje shi.

Buhari ya ce shi da kan sa zai zaɓi wanda zai gaje shi, ” abinda kawai nake buƙata shine goyon bayan ku gwamnoni.”

” Ina shekara ta ta karshe a zangon mulkina ta biyu, dole in maida hankali da jajircewa wajen tsayawa tsayin daka domin ganin Jam’iyyar APC bata kauce hanya ba.

” Akidun mu da turakun da muka kakkafa da suka rike jam’iyyar ba za mu bari su ruguje ba. Saboda haka dole mu hakura da juna mu yi abinda ya dace.

A karshe Buhari ya ce abinda jam’iyyar ta maida hankali akai yanzu shine mu ga mun yi nasara, kuma hakan na bukatar dole kowa ya ajiye burin sa ya zo gabaɗaya a yi abinda ya dace domin cigaban jam’iyyar APC.

Buhari zai dawo ranar Juma’ kwanaki biyu kafin babban taron jam’iyyar kamar yadda Premium Times Hausa ta ruwaito.

Leave a Reply