ADABI, Kano Ayau Hausa

Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Dr Abdallah Usman Gadon Ƙaya (حفظه الله)

Daga Ibrahiym A. El-Caleel
1. Akaramakallah, Assalamu alaikum. Fatan Malam yana cikin ƙoshin lafiya da albarkar rayuwa. Allah Ya saka da alheri bisa hidimar karantar da addini da ake yi kullun, amin.
2. Maƙasudin rubuta wannan wasiƙar shine don ankarar da Malam akan bidiyoyin shi da suke yawo inda yake yawan bada labarai iri-iri. Waɗannan báƙin labarai suna da ban mamakin ji, musamman kasancewar suna fitowa ne daga majlisin ilimi ko mimbarin Jumu’ah.
3. Tashar AfricaTV3 a shafin su na Facebook sun saki wani faifai na Malam, inda kake hakaito wani labari da kace wani ne ya baka shi, akan yadda ma’aikatan lafiya mata da maza suke mu’amalar banza tsakanin su a aikin dare, wato “night shift”.
4. Akramakallah, Allah ne Ya taimaki wannan al’ummar tamu. Mutane sun amince sosai da malamai saboda amana ta ilimi. Hatta ƴan siyasa sun gane ƙimar malamai a idanun mutane, don haka suke raɓar malamai don su sahhale su mutane su zaɓe su. Duk wannan yana nuna irin darajar malamai ne a idanun jama’a.
5. Duk mutumin da mutane suka amince mishi, to wani babban nauyi ne ya hau kanshi. Mutumin ya zama jagorar al’umma, ya zama abin koyi. Maganganun sa suna da matuƙar tasiri cikin al’umma. Ashe kenan dole irin wannan mutumi ya riƙa auna maganganun shi kafin ya furta su. Duk labarin da zai bada, to ya tabbatar da ingancin sa. Ko da labarin ƙarya ne aka bashi, in fa ya bada shi, to mutane da yawa zasu karɓi wannan labarin a matsayin gaskiya ne.
6. Labarin da Malam yace an bashi gameda fasiƙancin ma’aikatan lafiya cikin dare, labari ne da cikin sauƙi zai iya rusa al’ummar mu. Musulman Arewa an bar mu a baya a fannin boko. Don haka a shekarun baya muke fama da ƙarancin ma’aikata, ƙo’ina bamu da mutane. Hatta asibitoci. Komai ustazanci ko sheɗancin mutum, idan shi ko matar sa bata da lafiya, wani zabgegen ƙato ne, ma’abocin shirka zai duba shi ko matar shi. Malamai da jagororin mu suka nuna kuskuren mu, aka zaburar da mutane suka shiga boko sosai. Cikin ikon Allah yanzu mun fara samun sauƙi kaɗan. Ana samun mata musulmai sosai cikin ma’aikata lafiya. Don haka yanzu asirin matan mu ya fara rufuwa. Idan sun je asibiti da lalura, suna iya cin sa’a ƴan uwan su mata su duba su. Ka ga mutuncin matan mu ya rufu.
7. Malam, a halin yanzu fa su kansu ma’aiktan lafiya mata suna cikin ƙalubale. Mazaje na gudun auren su saboda ganin basu da wadataccen lokacin kula da yara da gida. Yanzu kuma da Malam yake hakaito labarin fasiƙanci da ake da sunan kwanan asibiti, to kamar fa Malam yana ƙara sanyawa ne a kyamaci auren ma’aikatan lafiya. Don haka duk Uba mai hankali, ba zai yarda ɗiyar sa ta karanta Medicine ko Nursing ba. Don kada ta gama ta kasa samun miji, kuma sannan a gari a riƙa mata kallon ƴar iska. Shima mijin ma’aikaciyar asibiti, yanzu an jefa mishi shakku ya riƙa zargin matarsa da cin amanar aure.
8. Wannan shine illar bada irin waɗannan labarai daga mimbarai na masallatan Jumu’ah, ko daga majalis na ilimi. Kuma saboda Allah, Akarakallah, shin kayi binciken wannan labarin da aka baka? Yanzu da fake news yayi yawa, don me mutum zai karɓi labari koma wani iri ne, sannan ya zo yayi gini akai, har yana sharhi?
9. Mu ƙaddara ma labarin nan tabbas gaskiya ne. A matsayin Malam, shin wannan hanyar da ya bi itace hanyar da za’a gyara mafsadar? Ai fasiƙi da fasiƙa ana samun su a ko’ina, ba sai cikin ma’aikata ba. Mata nawa ne suke zaune a gida basa aiki, amma kuma suke fasiƙanci a bayan idanun mazajen su? Shin hatta a nan Kano labarai nawa ne aka bada gameda matan aure mazauna gida waɗanda suke maɗigo a bayan idanun mazajen su? Don haka lamarin fa bashi da wani alaƙa da aikin asibiti, ko sharar titi ko zaman gida. Fasiƙi da fasiƙa duk inda suke basa fasa fasiƙancin su.
10. Ashe kenan hikima shine a cigaba da faɗakarwa game da zina, da zunubin cin amanar aure. Sannan a ja hankalin mata da maza da suke aiki da juna cewa su kiyaye haddin shari’ah. Su kiyaye amanar mazajen su da tarbiyyar iyayen su. A cigaba da waɗannan nasihohi akan kowa. Wannan shine zai taimaki al’ummah. Ba wai a jefawa mutane zargin wasu ƴan uwa da fasiƙanci ba.
11. Ina so Malam ya sani cewa ma’aikatan lafiya ma basa son aikin kwanan nan! Babu wacce zata yi naƙuda ta haifo yara sannan da daddare ta fi son zuwa “kwana da ƙarti” fiye da kwana da ƴaƴan ta. Basa so. Abin ya zama dole ne. Saboda mutane suna kamuwa da cuta cikin dare su buƙaci kulawa ta gaggawa; mata sukan shiga naƙuda da daddare. To idan yanzu babu musulmai mata irin mu a asibitocin, me aka yi kenan? Ai an koma gidan jiya kenan! Cikin daren Alaramma Ustaz Abu Fulan zai ɗauko matar sa Malama Ummu Fulan ya damƙa ta hannun Dr Samuel ya duba ta! Shi kuma wannan wani irin sharri kenan? Daga nan kuma wani irin labari Malam yake tunanin za’a fara kawo mishi daga asibitoci?
12. Sannan, na ga Malam yayi bidiyo yana gyara kalamansa cikin wancan labari. Wannan yayi kyau, duk da dai wasu sun ce Dr Abdalla yayi wannan ne saboda ƙungiyar ma’aikatan lafiya sun yi barazanar maka shi a kotu saboda yayi ƙoƙarin ɓata musu suna. Wannan dai shine matsalar da ake gudu. Irin wannan abin shine yake jawowa malamai raini. A ƴan shekarun nan Malam yayi ta fama da irin waɗannan matsaloli. Sai yayi magana, daga baya kuma sai ya janye ko yayi ƙoƙarin abinda bature ke cewa “damage control”. Akaramakallah, wannan abin anya ba zai taɓa girmar ka a idanun jama’a ba kuwa?
13. Da ace Malam zai tsaya iyakar gundarin ilimin da yake karantarwa, to da mun ce Alhamdulillahi. In ma labarin ne, Malam sai ya taƙaitu ga iya abinda shi da kanshi ya sheda. Saboda an hakaito wa Malam labarai da yawa waɗanda ƙarshe dai labaran nan suka jefa Malam cikin rikici. Ashe lokaci bai yi ba da Malam zai hana mutane kawo mishi labarai?
14a. Ina mai rufe wannan nasiha tawa da Hadisin Manzon Allah ﷺ da yake cewa, (كفى بالمرء كذبا أن يحدث بكل ما سمع).
14b. Al-Imam Abdurrahman bnul Jawziy (Rh) da yazo bayanin hadisin nan, sai yace:
‎(فيه تأويلان، أحدها: أن يروي ما يعلمه كذبًا، ولا يبينه فهو أحد الكاذبين، والثاني: أنَّ يكون المعنى بحسب المرء أن يكذب؛ لأنَّه ليس كلُّ مسموع يصدق به، فينبغي تحديث الناس بما تحتمله عقولهم)
16. Allah Ya ƙarawa Malam lafiya da albarka. Allah Ya taimake mu akan harsunan mu. Allah Ya kiyaye mana mutuncin mu.
Wassalatu wassalamu ala RasulilLah.
Naka a musulinci,
Ibrahiym

Leave a Reply