BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Ban ce zan rushe babban Masallacin Abuja ba – Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya karyata labarin da ake yadawa cewa yana shirin rushe wani sashe na Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja.

A maimakon haka, Ministan ya ce ya ba Shugaban Hukumar Raya Babban Birnin (FCDA) Injiniya Shehu Ahmed sa’o’i 24 ya yi masa jawabi a kan ainihin matsayin gwamnati kan rushe wani bangaren masallacin da kuma shirin biyan diyyarsa.

Hakan dai ya biyo bayan bukatar fadada aikin wata hanya da za ta wuce ta jikin masallacin, wanda hakan ya sa hukumomin shi suka nemi a biya diyyar shi.

Ministan dai ya bayar da umarnin ne lokacin da ya karbi jagororin kwamitin masallacin da ke karkashin Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, inda ya ce ofishinsa ba shi da niyyar kuntata wa wani addini.

Leave a Reply