Al’ajabi, Kano Ayau Hausa

Barayi sun bige da barci bayan sun yi sata a gidan wata tsohuwa

“Wasu matasa barayi, Sun Shiga Gidan Wata Tsohohuwa Bayan Sun Gama Kwashe Kaya Barci Ya Dauke Su Nan Take.”
“Majiyar Alfijir Hausa ya shaidawa jaridar cewa! Daman tsohuwar an dade anai mata sata a cikin gidanta, wani lokaci tsohuwar ta tsayu cikin dare tana fadawa Allah; da nufin Allah ya tona mata asirin masu yi mata wannan aika-aikan, a karshe dai Allah ya tona asirin su, bayan da barayin suka kamala kwashe mata kaya kaf.
“Hakan ya kara bude wata sabon fai-fai ne, ita kuma tsohuwar tana can tana sharara barci, nan take dai barayin sai suka bige da barci, barci kuma mai nauyin gaske, Wanda har sai da tsohuwar ta tashi da nufin za ta zaga ban daki aikuwa tsohuwar ta yi arba da wadannan barayin kwance share-share kowa da abinda ya kwashe gaban shi”
“Alfijir Hausa ya kara samun wasu bayanai daga majiyoyi cewa! Tsohuwar ‘Yar gata Ce a wurin Dan cikinta, inda Dan nata ya gwangwajeta da kayan alatu ta zamani, kama daga abin kallo ta zamani, rediyo, firiza da dai sauran nau’oin kayan wuta na ababdn more rayuwa”
Bisani sai tsohuwar taje tataso wani jikanta dake kwana a gidan daya zo yaga abin mamaki, inda nan take jikan nata ya kakkaftawa wadannan barayin wadannan hotunan da mai karatu yake kallo.
“Wannan al’amarin ya faru ne a wani gari da ake kira da BA’ASI ta jahar Oyo a tarayyar Najeriya”

Leave a Reply