Fitaccen mai shirya fina-finai a kuɗancin Najeriya ta Nollywood, Jim Iyke, ya musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta cewa ya musulunta, kamar yadda BBC ta ruwaito.
A ranar Laraba ne aka wayi gari da wannan labari da ke ta yawo a shafukan sada zumunta a Najeriya.
Sai dai adaidai lokacin da wasu Musulmi ke maraba da wannan batu, sai jarumi Jim Iyke ya fitar da sanarwa da ke cewa babu gaskiya a cikin wannan labari.
Jim Iyke da yanzu haka ake naɗar shirin fim dinsa, a wani bidiyo da ya fitar a shafinsa na Instagram ya ce ba shi da niyyar Musulunta.
Ya ce hotunan da ake ta yaɗawa kan ya musulunta shirin wani fim ne da ake naɗa a Ghana.