BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Ban fara wani shiri game da masarautun Kano ba-Abba Gida-Gida

Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya yi watsi da rahotan da ake yaɗa wa na cewa ya soma shirye-shiryen rushe Masarautun da Gwamnatin da ta shuɗe ta ƙirƙira.

A wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran Gwamnan Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce babu wani ɓoyayyen shiri tsakaninsu da yan majalisu kan masarautun.

Ya ƙara da cewa, duk abin da za su yi da Majalisar dokokin jihar za su yi shi ne a buɗe domin jama’a su shaida kamar yadda ya shaida wa Freedom Radio.

Leave a Reply