Kano Ayau Hausa, Siyasa

Babu wanda ya isa ya cire ni a Shugaban NNPP a Kano-Hisham

Shugaban NNPP na Kano ya yi barazanar zuwa kotu bayan da uwar jam’iya ta naɗa Doguwa a matsayin shugaban riƙo

Shugaban Jam’iyar NNPP a Jihar Kano, Hisham Habib, ya yi barazanar ɗaukar matakin Shari’a bayan da uwar jam’iyar ta ƙasa ta ta sauke shugabannin jam’iyar na jiha.

Daily Nigerian Hausa ta fahimci cewa NNPP ta samu haɓɓaka a arewa kwanaki kaɗan bayan da sanarwar ta fita cewa tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso na shirin barin PDP zuwa jam’iyar ta NNPP.

A jiya Laraba ne Habib ya yi maraba da zuwan Kwankwaso, sai dai ya ce babu tabbacin samun takara ga sababbin shigowa jam’iyar.

A wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis, Habib ya ce matakin na rushe shugabannin da uwar jam’iyar ta yi wani ƙarfa-ƙarfa ne ga dimokuraɗiyya.

Ya ce wannan matakin bai dace ba kuma ba a bi hanyar nuna domokraɗiyya na haƙiƙa ba.

Habib ya koka da cewa idan har ƴan siyasa za su riƙa shigo wa jam’iya su ture waɗanda su ke ciki, to lallai siyasa ta shiga halin tsaka mai wuya.

Sabo da haka, Habib ya ce ya fara tuntuɓa domin ɗaukar matakin Shari’a ko kuma ya fice ma da ga jami’yar.

Leave a Reply