Kano Ayau Hausa, Siyasa

Ba zan bar APC ba-Shekarau

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Sanatan kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau ya musanta labarin da a ke yaɗa wa cewa zai fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP ko NNPP.
A tuna cewa APC mai mulki a Kano ta dare gida biyu tun bayan zaben fitar da shugabannin jam’iya, inda ta tashe zuwa ɓangaren Gwamna mai ci, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da na Shekarau.
Tuni dai ɓangarori biyun su na kotu, inda dukkansu ke dakon hukuncin kotun ƙoli a kan shugabancin jam’iyar a jihar.
Sai dai kuma Sanata Shekarau, a wata sanarwar da ya wallafa a sahihi shafinsa na facebook a jiya Lahadi da daddare, ya bayyana cewa babu wani shiri da yanke yi na barin jam’iyar APC.
Ya ce, “Da ga safiyar jiya zuwa yammacin yau Lahadi 24 ga watan Afrilu 2022, na samu sakonni da ga wurare da yawa, suna tambayar matsayina dangane da halin da ake ciki a jam’iyyar mu ta APC”.
“Labaran da a ke yaɗa wa cewa ina shirin canza sheka zuwa wata jam’iyya ba gaskiya bane. Ni Sanata Ibrahim Shekarau, Sardaunan Kano ina nan a cikin jam’iyyar APC, babu wani shiri ko kulli a sarari ko a boye na shiga wata jam’iyya ta daban”.
“Ya kamata jama’a su sani jam’iyyar APC da ni aka yanke mata cibiya, kuma na yi aiki tukuru domin samun kafuwarta da nasararta. Yadda ake tafiyar da ita ne muke jayayya aka kai, kuma maganar tana gaban kotu. Har yanzu muna sauraren hukuncin karshe na kotun koli.”
“Ina fatan zaku ci gaba da yi mana addu’a ta alheri da fatan dorewar zaman lafiya a Kano da Najeriya.”
A makon da ya gabata ne dai akai ta yada labarin cewa Malam Ibrahim Shekarau yace Wai daga Abuja zai tsaya a na’ibawa Yan Lemo ,Wanda akai ta alakanta hakan da cewa jam’iyyar NNPP Mai kayan marmari yace shirin komawa,” in ji sanarwar kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.

Leave a Reply