BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Ba za mu dauki malamin jami’a da ke da ra’ayin siyasa aiki ba – INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce ba za ta tura duk wani malamin jami’a da ke da alaka da wata siyasa aiki a zabukan kasar da za a fara nan da ‘yan kwanaki ba.

Hukumar ta kuma ce duk wani malamin jami’a da zai yi mata aikin wucin-gadi a zabukan kasar da ke tafe dole ne ya yi rantsuwar ‘yan ba-ruwanmu, wato ba ya wata jam’iyya ko siyasa ko goyon bayan wani dan takara.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya sanar da haka jiya Alhamis a Abuja a lokacin wani taro da shugabannin jami’o’in kasar a Hukumar Jami’o’in Kasar (NUC).

Sai dai ya ce daman ita rantsuwar ta tabbatar da cewa mutum ba shi da wata jam’iyya ko dan siyasa ko takara da yake goyon baya, tana hawa kan dukkanin ma’aikatan zabe ne kamar yadda sashe na 26 na dokar zabe ta 2022 ya tanada.

Jaridar daily Trust ta ruwaito cewa, shugaban ya ce hukumar ba za ta tura duk wani malamin jami’a da ta san yana da alaka da wata jam’iyya ba.

“Haka suma wadanda watakila ba su shiga siyasa amma an san suna da dangantaka da wata siyasa ba za a dauke su ba. Hka suma wadnda aka yanke musu hukunci kan magudin zabe dole ne a ware su,” in ji shugaban na INEC.

Leave a Reply