GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Ba za a fuskanci karancin abinci a Najeriya ba – Gwamnatin tarayya

Ministan noma da raya karkara na Najeriya Mohammed Abubakar ya yi watsi da fargabar da ake yi a kasar na fuskantar karancin abinci cikin watanni masu zuwa.

Yayin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan majalisa a wajen kare kasafin kudin hukumarsa a zauren majalisar dokokin kasar, ministan ya ce ba za su bari hakan ta faru ba.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar dai sun bayyana cewa matsalar ambaliyar ruwa za ta shafi fannin noma a kasar.

Sun kara da cewa an yi hasashen cewar kasashen Afirka za su fuskanci karancin abinci sakamakon rashin shigo da abinci da yakin Ukraine ya haddasa.

To Amma ministan ya ce ”ba za mu bari matsalar karancin abinci ta yi tasiri a Najeriya ba, ina mai tabbatar muku da cewa da yardar Allah hakan ba za ta faru ba, saboda akwai matakai da dama da muka dauka domin magance wannan matsalar,” kamar yadda BBC ta ruwaito.

Ya ci gaba da cewa ”daya daga cikin matakan da muka dauka shi ne noman rani, wanda muka ware masa kudi, muna aiki da ma’aikatar kudi, muna kuma samun tallafi daga cibiyoyin kudi, kamar bankin raya kasashen Afirka, dan haka za mu fadada noman ranin”.

Ministan ya kuma ce gwamnati na nazari kan irin barnar da ambaliyar ta haifar wa amfanin gona kamar shinkafa da masara, da kuma yawan manoman da lamarin ya shafa. kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar (NAN) ya ruwaito.

Leave a Reply