Babbar jam’iyyar adawa ta APC a jihar Kano, ta soki tsarin tura dalibai karatu zuwa ƙasashen ƙetare domin yin karatun digiri na biyu a fannonin ilimi daban daban, inda tace daɓen kwalo ne kawai, domin babu bukatar hakan a halin yanzu.
Kakakin jam’iyyar, Ahmad S. Aruwa ne ya bayyana haka, inda yace anfi bukatar a inganta ilimin cikin Gida kafin a tafi ƙasashen ƙetare, saboda haka basu gamsu da wannan tsari ba, domin daga baya ma za’a iya jiyo koke-koken daliban akan batun kuɗin makaranta.
A ranar Juma’a ne dai rukunin farko na daliban da suka fita da sakamakon mafi kyau a karatun digirin farko yan asalin jihar Kano, suka tashi zuwa ƙasar India domin karatun digiri na biyu, wadanda gwamnatin Kano karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta dauki nauyin su.