BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Ba ni na kashe Ummita ba-Dan Chana

Dan Chana, Geng Quangrong da ake zargi da kashe Ummukulsum Sani a Kano cewa shi bai kashe ta ba.

A zaman da aka yi a watan baya, Dan Chanan ya ce yana so gwamnati da nema masa tafinta, saboda a cewarsa ba ya jin Turanci sosai.
Wannan ya sa Kwamishinan Shara’a na Kano, Musa Abdullahi Lawal ya nemo masa tafinta da zai rika masa bayani mai suna Mista Guo Cumru.
Sai dai bayan bayyana zarge-zargin da ake yi wa Dan Chana din, sai ya musanta duka zarge-zargen, inda ya ce bai kashe Ummita din ba.
Alkalin kotun sai ya dage shara’ar zuwa 16 ga Nuwamban bana domin cigaba da sauraron shara’ar.

Leave a Reply