Tshon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamiɗo ya ƙaryata rahoton da ya ce Dattawan Arewa da ‘yan takarar PDP na shugabancin ƙasa sun zaɓi tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi a matsayin ‘yan takarar da Arewa za ta tura wakilci a zaɓen fidda-gwanin PDP.
Jaridar Vanguard ce dai ta buga labarin cewa Dattawan Arewa sun tsayar da Saraki da Bala Mohammed ‘yan takarar su na zaɓen fidda-gwani wanda za a yi a ranar 28 Ga Mayu, 2022.
Jaridar ta ce wannan matsaya da suka ɗauka na ƙunshe cikin wata takardar bayan taro da dattijo Ango Abdullahi ya sa wa hannu, cewar Vanguard.
Sanarwar ta ce Dattawan Arewa ɗin sun zaɓi ‘yan takarar biyu daga cikin huɗun da suka miƙa sunayen su domin tantancewa.
Lamiɗo ya ce maganar gaskiya ba a taɓa zama an cimma wannan yarjejeniyar ba. Ya ce wannan dai ra’ayi ne kawai na wasu dattawan da suka fitar da sanarwar kawai.
“Shugabannin PDP masu ruwa da tsakin ta na Arewa ba su san da wannan magana wadda rahoton ta buga ba. Maganar wai wasu Dattawan Arewa sun zaɓi ‘yan takara biyu daga cikin dukkan ‘yan takarar Arewa da suka cancanta a PDP, don su tsaya zaɓen fidda gwani ba gaskiya ba ce.
“Bayan tuntuɓar shugabannin jam’iyya a jihohi 19 da Abuja da kuma mambobin jam’iyya, ina sanar da ɗimbin magoya bayan jam’iyyar mu da dukkan sauran jama’a cewa rahoton da kafar yaɗa labaran ta buga ra’ayin wani ne dai kawai wanda ya fitar da sanarwar, amma ba matsayar PDPn Arewa ba ce.” Haka Lamiɗo ya bayyana.
“Amma dai har yanzu ana nan mu na tattauna yadda za a cimma matsayar fitar da ɗan takara ɗaya ta hanyar yarjejeniya. Idan hakan ta yiwu, shikenan. Idan hakan bai yiwu ba kuwa, za mu tabbatar da an yi zaɓen fidda gwani a Gangamin PDP na Ƙasa.
“Matsayar da aka ce wai Dattawan Arewa sun ɗauka layani ce ga Arewa da kuma ‘yan takarar shugabancin ƙasa na Arewa a ƙarƙashin PDP.” Cewar Lamiɗo, wanda shi kaɗai ya rage a cikin jam’iyyar, daga cikin waɗanda su ka kafa ta. Sauran kuma daga waɗanda suka rasu, sai waɗanda suka canja sheƙa.