BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Ba hutu zan je a Landan ba- Shugaba Buhari

A ranar Alhamis ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa birnin Landan, a wata ziyara da fadarsa tace ta kashin kai ce.

Wata sanarwa da fadar shuganban kasar ta fitar ta ce Shugaba Buhari zai shafe kwana 10 a Landan kafin ya koma Najeriya.

Mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ya ce shugaban zai ringa gudanar da aiki daga can, domin kuwa ba hutu ya tafi yi ba.

Tuni dai Shugaba Buhari ya isa Landan din, inda wasu hotuna da mai ba shi shawara kan kafafen sada zumunta Bashir Ahmad ya wallafa a Twitter, suka nuna lokacin da shugaban ya isa Landan din.

Tafiyar shugaban dai ta jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan Najeriya inda suka rika bayyana ra’ayoyinsu a shafukan sada zumunta musamman Facebook da Twitter.

Mutane da dama na ganin cewa shugaban ya je ganin likitoci ne kamar yadda ya saba, amma fadarsa ta musanta hakan.

Mallam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa ziyarar tafiya ce ta kwana 10 ce don gudanar da wasu harkokin kashin kansa da ba su shafi aikin ofis ba.

Leave a Reply