GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Anya yajin aikin ASUU yana damun ‘yan siyasarmu kuwa?-Ahmed Musa

Shaharraen dan wasan kwallon kafan Najeriya, Ahmed Musa, ya kalubalanci ‘yan siyasar Najeriya kan yadda suke tura ‘ya’yansu karatu a kasashen waje duk kuwa da yadda yajin aikin malaman jami’o’i ya ki ci ya ki cinyewa a Najeriya.

Tun a watan Fabrairu ne daliban Najeriya ke zaune a gida, sakamakon yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ke yi, duk da ikirarin Gwamnatin Taryya na cewa akwai alamun nasara a tattaunawarta da su, kamar yadda muka kalato daga Aminiya.

To sai dai a ranar Litinin, Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya ce tura ta kai bango a yajin aikin, don haka lokaci ya yi da ya kamata su janye yajin aikin don daliban su koma karatu, ala bashshi sa dawo a ci gaba da tattaunawar da aka fara.

Amma a ranar Talata Ahmed Musa ta shafinsa na Instagram ya wallafa cewa abin kunya ne abinda ‘yan siyasar kasar nan ke yi na yada hotunan ‘ya’yansu da ke karatu a kasashen duniya, yayin da na talakawa a Najeriya ke jibge a gida sakamakon yajin aikin ASUU.

Ya ce: “Ga ‘yan siyasarmu, Yaya kuke ji idan kun ziyarci ‘ya’yanku da ke karatu a waje kuna yadawa, alhalin ASUU na yajin aiki? Hakan daidai ne a idonku? wannan fa na haska ku kanku ba ku yarda da tsarin da kuke jagoranta ba.

“Don Allah ku nuna min ‘yan kasar waje da ke karatu a jami’o’in Najeriya. Wannan bai isa ya tausasa zuciyarku ba? Kuma ku dawo matasan su fito suna muku bambadanci”.

Wannan kalamai nasa na zuwa ne bayan hotunan dan gidan Gwamnan Ribas, Nyesom Wike da ya kammala karatu a kasar Ingila sun karade kafafen sada zumunta.

Baya ga Gwamna Wike dai wasu Gwamnoni biyu sun halarci bikin kammala karatun dan nasa da suka hada da na Abia Okezie Ikpeazu da kuma takwaransa na Oyo, Seyi Makinde.

Tuni dai wasu kungiyoyi da dama a kasar nan suka yi barazanar shiga yaji aiki da zanga-zangar bai daya ta kasa, don nuna goyon bayansu ga ASUU.

Leave a Reply