BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Ana zanga-zanga kan batun Zainab Aliyu a Kano

Wasu dalibai suna gudanar da zanga-zanga neman sakin ‘yar Najeriyar nan da ke tsare a kasar Saudiyya, Zainab Aliyu.

Daliban suna gudanar da zanga-zangar ne a ranar Talata a Kano, inda masu zanga-zangar suka sakinta ba tare da wani ba ta lokaci ba.

A ranar Litinin ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Shari’a Abubakar Malami da ya shiga maganar Zainab Aliyu.

Jami’an tsaron Saudiyya sun kama Zainab Aliyu ne jim kadan bayan sun isa Saudiyya don yin aikin Umara ita da mahaifiyarta Maryam da kuma ‘yar uwarta Hajara kamar yadda BBC ya ruwaito.

Sun zarge ta da safarar kwayar Tramadol har guda 2,000 bayan da aka ga kwayoyin a wata jaka mai dauke da sunanta.

Amma tuni hukumar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi ta NDLEA ta bayyana cewa wasu ma’aikata ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano (MAKIA) suka saka mata kwayar a jakarta.

Kwamandan hukumar mai kula da MAKIA Ambrose Omorou ya tabbatar wa da BBC cewa tuni suka kama mutum shida, wadanda ake zargi da aikata hakan.

Leave a Reply