GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Ana sa ran zuwa Juma’a a janye yajin aikin ASUU

Shugaban kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya, ASUU, Farfesa Victor Emmanuel Osodekeya ce nan ba da jimawa za su koma azuzuwa domin ci gaba da koyarwa.

Ya bayyana haka ne yayin da ya gana da kakakin majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ranar Litinin.

Farfesa Osodeke ya yaba wa matakin da majalisar wakilan kasar ta dauka na shiga tsoma baki domin ganin an yi sulhu tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU wadda ta kwashe wata takwas tana yajin aiki.

Wani bidiyo da aka wallafa a shafin Tuwita na majalisar wakilan Najeriya ya nuna Farfesa Osodeke yana cewa sun kusa kawo karshen yajin aikin.

Bayan kammala zamansu din, ASUU ta umarci bangarorin kungiyar da ke jihohi da su zauna ranar Laraba, sannan su aiko da sakamakonsu ranar Alhamis, inda su kuma za su zauna su fitar da sakamakon karshe.

Leave a Reply