BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

An soke dokoki 16 na shari’ar Musulunci a Malaysia

Kotun tsarin mulki a Malaysia ta soke wasu dokokin shari’ar Musulunci 16 a jihar Kelantan da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Dokokin sun haɗa da hukuncin luwaɗi da cin zarafin mutum ta hanyar lalata da caca da kuma muzuntawa ko lalata wurare masu tsarki ko na ibada.

Kotun ta ce jihar ba ta da hurumin da za ta yi doka a kan harkokin da suke ƙarƙashin iko ko dacewar majalisar dokokin tarayya.

Hukuncin zai iya shafar dokokin shari’ar Musulunci da aka amince da su a wasu jihohin da Musulmi ke da rinjaye a ƙasar ta Malaysia, inda bin tsarin Musulunci sau da kafa, da ke ƙaruwa ke zama ƙalubale ga gwamnatin haɗakar ƙasar ta kabilu daban-daban.

Firaminista Anwar Ibrahim, ya ce ba hannun gwamnatin tarayya a hukuncin da kotun ta yi.

Leave a Reply