BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

An sauke Ali Baba Fagge daga Shugaban Dattawan APC

Kwamitin Dattawan jam’iyyar APC reshen karamar hukumar Fagge a jihar Kano, (Caucus) sun dakatar da shugabansu, SA Ali Baba Agama Lafiya Fagge bisa zarginsa da danne musu haƙƙoƙinsu da yayi har karo biyu.
Cikin wata takarda mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na kwamitin da mataimakinsa, Salisu Shitu da Shehu Sani Chidozie, da aka aikewa shugaban karamar hukumar Fagge, Ibrahim Muhammad Shehi, sun bayyana cewa Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya basu Naira Miliyan daya (N1,000,000) da Sallar da ta gabata ta hannun dakataccen shugaban nasu, amma shiru bai basu ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa, kwanan nan ma jam’iyya ta basu Motoci guda Ashirin domin halartar taron zuwan dan takarar shugabancin Nigeria na Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, na ziyarar kwanaki biyu da yayi a Kano, shima dai shiru bai basu haƙƙin su ba.
A baya dai cikin shekarar 2020 (Ranar Arfa) aka zargi mai baiwa Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje shawara akan harkokin addinai, Ali Baba Agama Lafiya Fagge, da saka dansa Huzaifa Ali Baba, ya karbe kudi N50,000 da gwamna ya bawa malamai na addu’ar Allah ya kawar da kwarona da kuma nemawa Kano zaman lafiya, ya basu N5,000 kowannensu, dukda kashedin da gwamna yayi akan kada wanda ya karbi wani kaso cikin malaman, amma Ali Baba yayi burus saida ya karba, kamar yadda muka kalato daga Nasara Radio.
Ali Baba ya amsa wannan zargi tun a wancan lokaci, amma yace anyi hakanne don a fadada abin, kasancewar akwai wasu malaman da sukayi addua a gida, kuma dama a haka aka tsara za’a basu cikin kudin da aka bawa wadanda suka je gidan gwamnati, abinda yasa shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano na wancan lokacin, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, yayi sammacin Ali Baba da dansa Huzaifa, kuma aka dawowa da malaman kudinsu, dukda da dai babu wani matakin doka da aka dauka akansu.

Leave a Reply