Al’ajabi, Kano Ayau Hausa

An sake kai wa rundunar tsaron Buhari hari, an kashe sojoji

’Yan bindiga sun kai hari kan sojojin rundunar da ke tsaron shugaban kasa inda suka kashe wani hafsa da wasu kananan sojoji a Abuja.
Jaridar Aminiya ta ce sojojin da ke cikin rundunar “7 Brigade Guard Nigerian Army” na kan hanyarsu ne ta komawa bayan sun kammala kai dauki a makarantar koyon aikin lauya da ke Abuja, inda ‘yan bindigar suka yi musu kwantan bauna, suka harbe soja mai mukamin kyaftin da sojoji biyu.
Labarin hakan ya fara fitowa ne kimanin sa’o’i 24 bayan ’yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun yi barazanar sace  shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai.
Lamarin ya faru tun a ranar Lahadi, amma jaridar Aminiya ta ce an samu jinkirin fitar labarin sakamakon yadda jami’an gwamnatin suka yi kokarin rufe labarin.
A farkon watan Yuli, ‘yan bindiga suka fara kai wa ayarin shugaban Nijeriya hari, inda suka bude wa tawagar Buharin wuta a kan hanyarsu ta zuwa Daura, jihar Katsina domin share fagen zuwan shugaban a mahaifarsa.

Leave a Reply