Daga karshe, an nada Shahararren ‘dan Bindiga Ado Aleru a matsayin Sarkin Fulani na Masarautar Yandoton Daji a Jihar Zamfara.
An gudanarda nadin sarautar da misalin karfe 3:30 na yammacin Jiya Asabar 16 ga Yuli, 2022.
Ado Aleru shi ne shugaban wata daba ce ta ‘yan bindiga da ke addabar al’ummar Katsina da Zamfara.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta bayyana neman sa a shekarar 2019 tare da bayarda kyautar Naira miliyan 5 ga wanda ya kawo shi ko ya bayarda labari inda za’a same shi.
Copied
Mugira Yusuf