A yau Juma’a ne Kotun Shari’ar Musulunci da ke unguwar Magajin Gari, Kaduna ta mika karar da aka shigar kan cin amana da yaudara a kan fitacciyar jarumar Kannywood Hadiza Aliyu-Gabon zuwa babbar kotun Shari’a a jihar.
Alkalin kotun, Isiyaku Abdulrahman ne ya mika karar zuwa babbar kotun shari’a da ke Tudun Wada, biyo bayan roƙon lauyan mai kara, Nurudeen Murtala.
Yayin mika karar, alkalin ya zargi lauyan da son bata lokacin kotun.
“Kuna da zaɓuɓɓuka biyu. Daya shi ne in soke karar ko kuma in sauya ta zuwa wata kotun,” in ji alkalin.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa Bala Musa, wani ma’aikacin gwamnati ne ya maka jarumar a kotu saboda ta ki aurensa.
Musa ya shaida wa kotun cewa, “Ya zuwa yanzu na kashe mata Naira dubu 396,000. Duk lokacin da ta nemi kudi nakan ba ta ba tare da wata damuwa ba, tare da fatan za mu yi aure”.
Wacce ake karar, wacce ta yi magana ta bakin lauyanta, Barista Mubarak Sani, ta musanta sanin Musa, ta na mai cewa ba ta taba ganinsa ko haduwa da shi ba kuma ba ta da wata alaka da shi.
Lauyan wanda ya shigar da karar ya gabatar da kwafin takardar banki ga kotun kuma ya shaida wa kotun cewa wasu mutane hudu ne suka karbi kudin da aka ce an aika wa wacce ake kara.
Biyu daga cikin hudun, Fatima Abdullahi da Abdullahi Yusuf sun yi ikirarin cewa aminan wacce ake kara ne kuma hadimanta ne.
Sai dai kuma sun amsa laifinsu na amfani da sunan jarumar wajen karbar kudi, inda su ke rokon kotu ta gafarta musu.
A takaice dai bayan kammala shari’ar, lauyan Gabon ya shaida wa manema labarai cewa suna bukatar kotu ta sallami wacce ya ke karewa saboda ba ta yi zamba ba ko kuma ta ci wa wani amana kamar yadda ake tuhuma a baya ba.
Lauyan wanda ya shigar da karar a daya bangaren ya ce adalci ne kawai ya ke so.