BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

An kirkiri na’urar mutuwa cikin sauki

Mutane da yawa suna sha’awar rayuwar Turawa, rayuwar da ba Allah a cikinta, sai zallar duniya, wanda hakan yake jawo musu hauka iri-iri. Ban ce dukkaninsu ba su da hankali ba, amma akan samu waɗanda tunaninsu yake ƙuntace.

A nan wata na’urar kashe kai ce da aka samar da ita daga ƙasar Switzerland, wadda hukumomin ƙasar suka amince da a fara aiki da ita., kamar yadda muka kalato daga The Daily Reality Hausa.

Wani abin mamaki shi ne, ita ƙasar ta Switzerland ƙasa ce mai yawan albashi da kayan more rayuwa da kuma uwa-uba tsafta. Hatta a cikin ƙasashen nahiyar Turai, ita ta daban ce. Amma duk da haka tana daga cikin ƙasashen da ake yawan samun kashe-kashen kawuna.

Leave a Reply