Alhaji Tukur Mamu, jagoran masu sasantawa tsakanin ‘yan bindiga da fasinjojin da aka yi garkuwa da su a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan Maris, an kama shi a birnin Alkahira, babban birnin kasar Masar, tare da iyalansa.
Daily Nigerian Hausa ta ruwaito daga Daily Trust cewa, Mamu wanda ke kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin ummara, an tsare shi na tsawon sa’o’i 24 a filin jirgin sama na Alkahira, kuma ana shirin dawo da shi gida Nijeriya.
Da ya ke zantawa da Daily Trust, Mamu ya ce ya bar Najeriya ne a ranar Talata, kuma bayan da jami’an tsaron Masar suka bincike shi, ba a gano wani abu na laifi a tare da shi ba.
Mamu ya yi zargin cewa wanii shiri ne na gwamnatin Najeriya na tsare shi a wata ƙasa, kamar yadda aka yi wa ɗan gwagwarmayar ƴancin Yarabawa, Sunday Igboho, amma hakan bai samu nasara ba ba saboda gwamnatin Masar din ta gano cewa takardunsa basu da matsala ne.
Daily Trust ta ruwaito cewa Mamu ya cire hannunsa a tattaunawar da ƴan bindigar bayan ya yi zargin cewa gwamnatin Najeriya na yi masa barazana da kuma yunkurin ɓata masa suna.
Har yanzu gwamnati ba ta mayar da martani kan ikirarin Mamu ba amma wasu na zarginsa da haɗa baki da ƴan ta’adda, zargin da ya musanta.