Kano Ayau Hausa, Labarai

An kama mabarata a Saudiyya

Hukumomin tsaro a Saudi Arebiya sun sanar da kama ƴan ƙasa da masu karya doka, har da ma wasu masu barace-barace a Masallacin Harami na Makka.
Hukumomin sun baiyana cewa sun kama wani ɗan ƙasar india da ya ke marairaice wa masallata domin su bashi sadaka, inda su ka kame wani ɗan ƙasar Morocco ya na bara kai tsaye, dukkan su a Masallacin Harami na Makka.
Sun ƙara da cewa sun kama wani ɗan Yemen da ya ke basaja da sandar guragu, a zuwan shi gurgu ne domin a bashi sadaka.
Hakazalika, hukumomin sun ce sun kama wani mahaifi yana basaja da ɗan sa da ya ɗora a kan keken guragu cewa bashi da lafiya domin a basu sadaka, amma da a ka kama shi, sai a ka ga ɗan nasa lafiyayye ne.
Hakan na zuwa ne bayan da Saudi Arebiya ta saka dokar mai karfi ta hana bara.
Tuni mahukunta a ƙasar su ka fara kamen mabarata a wani matakin na tabbatar da hana karya dokar hana barace-barace ta ƙasar.
Duk wanda a ka kama ya na barace-barace da makamantan irin waɗannan laifukan sai an ɗaure shi shekara ɗaya a gidan yari ko kuma ya biya tarar Riyal dubu 100.
Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewa waɗanda hukumomin su ka kama na bara ba ƴan Nijeriya ba ne, saɓanin rahotanni da ke fitowa a shekarun bayan cewa ƴan Nijeriya, musamman Hausa wa na zuwa Saudiya domin yin bara su samu kuɗi.

Leave a Reply