Babbar kotun jiha, karkashin jagorancin mai shari’a, Sanusi Ma’aji, ta sanya ranar 26 ga wata, domin fara sauraron karar da aka shigar gabanta, na kalubalantar rushe shugabancin jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano, tare da tabbatar da Umar Haruna Doguwa, a matsayin shugaba.
Hishan Habib, shi ne wanda ya shigar da karar, a da’awarsa na cewar shi ne halattaccen shugaban jam’iyyar a Kano, kuma ya dauki tsawon lokaci yana fadi-tashi akan jam’iyyar, saboda haka yake ganin bai kamata uwar jam’iyya tayi masa haka, kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto, kamar yadda Nasara Radio ta ruwaito.