BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

An gano gidan haihuwar jariran sayar a Nasarawa

Rundunar ‘yan sanda a jihar Nasarawa da ke ta ce ta gano gidan da ake zargin sayar da jarirai a karamar hukumar Karu ta jihar.

BBC Hausa ta rawaito cewa rundunar ta ce ta ceto mata shida da kuma jariri ɗan wata shida a gidan.

A sanarwar da ya fitar, jami’in hulda da jama’a na yansandan jihar, DSP Ramhan Nansel ya ce da misalin 2 na rana su ka kai samame Karu bayan samun wasu bayanan sirri, kamar yadda muka kalato daga Daily Nigerian Hausa.

Ya ce ana basaja da gidan ne a matsayin gidan kula da marayu. Sai dai bincike ya gano cewa ana garkuwa da kananan yara ana yi musu ciki sannan a sayar da jariran da suka haifa.

An dai cafke wasu mutum uku da ake zargin ke aikata wannan muggun aika-aika.

Leave a Reply