Al’ajabi, Kano Ayau Hausa

An fi kashe Musulmi a yakin Boko Haram-Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaida wa kafafen watsa labarai cewa akasarin mutanen da mayakan Boko Haram suka kashe Musulmai ne, yana mai cewa burin ‘yan kungiyar shi ne su yi amfani da addini wajen raba kan ‘yan kasar.

A wata makala da ya rubuta wadda aka wallafa a Jaridar Christianity Today, Shugaba Buhari ya ce bai kamata a kyale mayakan Boko Haram su raba kan ‘yan Najeriya ba, kamar yadda BBC ta ruwaito.

“A hakikanin gaskiya, kashi 90 cikin 100 na mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa Musulmai ne: cikinsu har da ‘yan makaranta mata Musulmai 100 wadanda aka sace tare da takwararsu Kirista guda daya, da kai hare-hare a masallatai da kuma kashe fitattun Malaman addinin Musulunci.”

“Wadannan ‘yan ta’adda suna so su gina katanga da za ta raba tsakaninmu. Sun gaza a yunkurinsu na hare-haren ta’addanci, don haka yanzu suna so su raba kanmu ta hanyar sanya mu sukar juna.”

Shugaban kasar ya rubuta makalar ne domin yin jaje da alhinin kisan da wasu da ake zargi mayakan Boko Haram ne suka yi wa wani limamin Kirista, Rabaran Lawan Andimi bayan da suka sace shi.

An halaka Lawan Andimi ne a karamar hukumar Michika ta jihar Adamawa bayan an yi garkuwa da shi a farkon watan Janairun wannan shekara a wani hari da ‘yan Boko Haram suka kai a kauyensu.

Kwanaki kadan bayan da aka yi garkuwa da shi an ga marigayin, a wani bidiyo da ‘yan kungiyar Boko Haram din suka saki, yana rokon gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya ceci rayuwarsa.

Leave a Reply