BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

An Bude Asusun Bankin Hukumar Hisbah

Bayan rufe asusun Bankin Hukumar Hisbah ta jahar Kano.

Banban Kwamandan Hisbah Sheikh Aminuddeen Ibrahim Daurawa ya umarci Babban Daraktan hukumar Alhaji Abba Sa’id Sufi da ya nemi ba’asi akan dalilin rufe asusun Bankin hukumar.

Ba tare da bata lokaci ba Babban Daraktan hukumar Alhaji Abba Sa’id Sufi ya tuntubi ma’aikatar shari’a domin samun shawarwari akan lamarin.

Washegari bayan Babban Kwamandan Hisbah Sheikh Aminuddeen Ibrahim Daurawa ya yi hira da kafar yada labarai ta TRT Hausa akan lamarin Bankin ya fahimci kuskuran da ya yi na rashin rubutawa hukumar Hisbah cewar Kotu ta umarcesu ne da kwarya-kwaryar hana taba kudinta da bai gaza N800,000 ne ba kawai.

Amma sai suka yi kuskuran rufe asusun gaba daya maimakon kwarya-kwaryar hana taba asusu na kudi N800,000 kawai. Daga bisani washegari suka bude asusun bankin ba tare da bata lokaci ba bayan sun fahimci kuskuransu kuma suka nemi afuwan hukumar.

Rufe asusun bankin hukumar ya biyo bayan wani sumamen da hukumar ta yi a wani otal dake Sabon Gari a shekarar 2019 wanda kungiyar masu Otal suka gurfanar da hukumar a gaban kotu wanda baya rasa nasaba da irin ayyukan da hukumar take yi na umarni da kyakkyawa da hani da mummuna.

Koma menene hukumar ba za ta fasa gudanar da ayyukanta ba a bisa doka da oda kamar yadda ta saba.

Leave a Reply