Hukumomi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun ƙaddamar da dokar ta-ɓaci game da satar waya da kuma wasu laifukan da ake aikatawa a birnin.
Kafofin yaɗa labarai sun ce majalisar dokokin jihar ta nuna damuwa kan matsalolin satar waya da sane da shan miyagun kwayoyi da ma waɗansu laifukan da ke barazana ga zaman lafiyar jihar.
A wata mahawara da shugaban masu rinjaye na majalisar ya gabatar, ‘yan majalisar sun amince kan cewa akwai buƙatar a gaggauta magance matsalar kafin ta yi ƙamari.
Majalisar dokokin ta kuma amince da wani ƙuduri da ya buƙaci gwamnatin jihar ta dauki dukkan matakan da suka kamata domin hukunta waɗanda aka kama da laifi.