Allah Ya yi wa tsohon Gwamnan Arewa ta Tsakiya Birgediya Abba Kyara rasuwa bayan ya yi fama da jinya, inda ya rasu yana da shekara 80 a duniya.
Shi dai Abba Kyari ya zama gwamnan Arewa ta tsakiya ne a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa na mulkin Soja, janar Yakubu Gowon, daga ranar 28 ga watan Mayu zuwa watan Yuli na shekarar 1975. A shekarar 1967 ne janar Yakubu Gowon ya samar da jihohi goma sha biyu a Najeriya bayan ya rushe shiyyoyin Arewa da na Kudancin Najeriya, inda a cikin shiyya Arewa kadai sai daya samar da jihohi guda shida, daga cikinsu akwai jahar Arewa ta tsakiya, wanda daga bisani aka canja mata suna zuwa Kaduna a shekarar 1976. Abba Kyari ya gaji tsohon gwamnan Arewa, Birgediya Hassan Usman Katsina, yadda abin ya faru kuwa shine a shekarar 1966 wasu kananan Sojoji yan kabilar Ibo suka yi juyin mulki ta hanyar kashe Sardauna Tafawa Balewa, shugaban shiyyar yammacin Najeriya da kuma sauran manyan Sojoji yan Arewa.