BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Akwai guraben aiki sama da dubu 100 da Buhari ya hana dauka

Wani dan Majalisar dokokin tarayya a Najeriya ya ce akwai guraben aikin gwamnatin tarayya sama da dubu ɗari da ashirin amma shugaban kasar Muhammadu Buhari ya hana a cike su.

Honorabul Sani Bala Tsanyawa, wanda shi ne shugaban Kwamitin kula da Ayyukan gwamnati na Majalisar Wakilan Najeriya ne ya tabbatar da hakan a hirarsa da BBC Hausa.

Ya ce tun a shekarar 2019 ne Shugaba Buhari ya sanar wa majalisar dokoki ɗaukar matakin a lokacin da ya je zaurenta domin gabatar da kasafin kuɗi.

Ya ce tun da shugaban ƙasar ya sanya wannan haramci ba a ƙara ɗaukar aiki ba a irin waɗannan ma’aikatu.

Sai dai a cewarsa an bai wa wasu ma’aikatun gwamnatin damar daukar ma’aikata saboda dalilai masu ƙarfi.

Bangarorin da aka yi wa rangwamen sun haɗa da na tsaro da lafiya – sakamakon barkewar annobar korona.

Ya kara da cewa “Daga shekara biyar a baya zuwa yau, bincikenmu ya nuna cewa ma’aikata dubu ɗari da talatin ne suka bar aiki.”

“Wasun su ko dai sun mutu, wasu kuma sun yi ritaya, wasu kuma sun samu wani aikin na daban sun bar na gwamnatin tarayya.” kamar yadda BBC ta ruwaito.

Leave a Reply