BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Abubuwan da za a rika tuna ni da su bayan 2023-Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nanata kudurinsa na tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zabe a kasar a 2023.

Shugaban ya fadi hakan ne a jawabin bankwana da ya yi a taron Majalisar Dinkin Duniya da ake yi birnin New York na Amurka.

”A matsayina na Shugaba, daya daga cikin tarihin da nake son bari shi ne na ga cewa an gudanar da sahihi kuma tsabtataccen zabe. Ta hakan ne ‘yan Najeriya za su zabi shugabannin da suke so,” in ji Buhari.

Ya kara da cewa wanda duk zai gaje shi zai gudanar da jawabi a madadin Najeriya a taron majalisar na gaba.

”A yanzu muna shirin gudanar da babban zabe a Najeriya a watan Fabrairun badi. Saboda haka a taron Majalisar Dinkin Duniya na 78, za ku ga sabuwar fuska ne a kan wannan munbari”, a cewar Shugaba Buhari kamar yadda BBC ta ruwaito.

Ya kuma yi magana a kan rawar da kasarsa ta taka wurin ganin an mika mulki salun alun a wata gwamnatin dimokradiyya a Gambia.

Shugaban zai kammala wa’adin mulkinsa karo na biyu a watan Mayun badi, inda zai mika mulki ga sabuwar gwamnati.

Leave a Reply