‘Yan Nijeriya suna ci gaba da jiran sunayen mutanen da Shugaba Bola Tinubu zai nada a matsayin sabbin ministocinsa, duk da cewa saura kasa da kwana 20 wa’adin da doka ta dibar masa don ya yi hakan ya cika.
Sai dai idan aka yi la’akari da sunan da ‘yan kasar da suka sanya masa na “Baba Go Fast,” wato shugaban da ke da zafin-nama wajen daukar mataki, kamar yadda ya nuna a farkon hawansa wajen daukar wasu zafafan matakai, wasu suna ganin lokaci ya yi da ya kamata shugaban ya kafa majalisar ministocinsa.
Ko da yake Shugaba Muhammadu Buhari a wa’adinsa na farko a shekarar 2015, sai da ya kwashe kusan wata shida kafin ya nada nasa ministocin.
Wasu suna ganin Shugaba Tinubu ya bambanta da Buhari ta fuskar zafin-nama, misali a ranar da aka rantsar da shi ya sanar da cire tallafin mai wanda gwamnatocin da suka gabace shi suka kasa yi.
Bayan ‘yan makonni kuma ya sanar da dakatar da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) Godwin Emefiele da kuma Shugaban Hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa da Shugaban Hukumar Kwastam Hameed Ali da kuma sauke manyan hafsoshin tsaron kasar.
‘Tinubu yana da sauran lokaci’
Babban Mai Taimaka wa Shugaba Tinubu kan hulda da ‘yan jarida Malam Abdulaziz Abdulaziz ya shaida wa TRT Afrika cewa babban abin da Shugaba Tinubu ya sanya a gaba tun bayan dawowarsa daga Guinea-Bissau a ranar Litinin shi ne “tattara sunayen ministocin da zai nada.