BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Abin da na fahimta bayan na je Iran

Daga Dr Ahmad Gumi

FASSARA DA SUMMARY Daga Mustapha Ja’afar

Munyi awoyi 27 muna tattaunawa da malamai na mazhabobi daban-danan daga kasashe fiye da 100.

Tsantsar gaskiya shugaban Iran ya fadi a wajen. Kuma yayi alkawarin ci gaba da taimakon Palasdinawa da ire-iren su, a aikace, masu tunkarar kalubalen da yankin Middle East yake fuskanta.

Mafiyawan shuwagabannin kasashen duniya basu da wannan jarumtakar; suna fifita maslahar su ne akan ta addini.

Taron ya shawarci kasashen musulmai su hada kai a tsakanin su da kuma kawayen su wajen kwato ma Palasdinawan hakkin su.

Kasar Iran tafi sauran kasashe musamman na Larabawa mutunta malamai da basu matsayin su a cikin jagorantar al’umma. An taba gayyata ta taron zaman lafiya na duniya a America amma sai aka hana ni VISA. Kun san dalili ai!

Naso ace nayi ma Iran wasu tambayoyi. Amma na gane cewa tana bukatar canza salo a alaqar ta da sauran kasashe a siyasance da kuma ta fuskacin tattalin arziki.

Iran tana da tsohuwar wayewa kamar Egypt shi yasa ta iya fuskantar danniyar tsarin siyasa da tattalin arzikin duniya kuma shi yasa ya wajaba ta gyara alakarta da kasashen Larabawa da na Africa har a bangaren kasuwanci.

Musulman duniya musamman Ahlussunnah suna kyamar Iran ne saboda zagin Sahabbai. A wajen taron shugaban Iran da sakataren taron sun yi ma Sahabbai addu’a tare da girmama su. Sunnah da Shi’a zasu iya girmama abinda junansu suke girmamawa sai su hada kai akan tattalin arzikinsu da zamantakewar su irin yanda suke alaqa da Turawa masu kare masu zagin Manzon Allah a kasashen su.

Na yaba ma Iran akan juriyar ta game da siyasar duniya, da yunkurin karya ta da ake yi, da kokarin kusanto da mazhabobi a junansu da take yi game da matsalolin da suka shafi duka al’umma. Wannan karantarwar Musulunci ne”-DR. GUMI

Ina fata nayi adalci kuma nayi dai-dai wajen fassara da paraphrasing na rubutun da Dr. Gumi yayi; Ina fata ban canza mashi sako ba. A Shari’ar Musulunci, a yaki da siyasa, maslaha ake dubawa! Wani lokaci da kafiri zaka hada kai!

Leave a Reply