Kano Ayau Hausa

Abba Gida-Gida ya biya wa daliban Kano kudin NECO

Gwamnatin Jihar Kano ta kashe Naira Biliyan 1.5 wajen biyan kudin rajistar jarrabawar NECO na ɗalibai dubu 57 na Makarantun Sakandare daban-daban na Jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran mataimakin gwamnan jihar, Aminu Gwarzo Ibrahim Shuaibu ya fitar a Kano.
Ya ce gwamna Abba Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin buɗe fara zana jarabawar a makarantar Rumfa College da ke cikin birnin Kano.
Gwarzo, wanda ya wakilce gwamna Yusuf, ya lura cewa biyan kudaden na daga cikin manufofin gwamnatinsa na farfaɗo da ilimi a jihar.
Ya kuma bukaci daliban da suka amfana da su bada dage domin samun sakamako mai kyau a jarrabawar domin tabbatar da dimbin jarin da gwamnati ta saka a harkar neman ilimi.
A nasa jawabin, kwamishinan ilimi, Umar Haruna Doguwa ya bayyana cewa jihar ta kafa kwamitin tantance makarantun kwana da aka rufe su da nufin bude su.
Ya yabawa gwamnatin jihar bisa inganta shirinta na ciyar da makarantu, inda ya ce nan ba da dadewa ba za a samar da karin bencina da tebura ga makarantun.

Leave a Reply