BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

A rage albashin ‘yan majalisa a ba ASUU-Ndume

Sanata Ali Ndume ya shawarci gwamnatin tarayya ta zabtare albashin ‘yan majalisa da kashi 50 cikin 100 domin biyan malaman jami’o’i da ke yajin aiki kuɗaɗensu.

Sanata Ndume da ke wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattijai ya shaida hakan ne a birnin Maiduguri lokacin wani taro.

Jaridun Najeriya sun rawaito sanatan na cewa wannan abu ne da ya shafi kasa baki ɗaya, kuma dole a wasu lokutan a ɗau matakan ceto ‘yan kasa da ilimi, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Kiran da sanatan ya yi na zuwa ne adaida lokacin da malaman jami’i’oi ke korafin cewa rabin albashinsu aka basu bayan sun janye yajin aiki.

Dan majalisar dai na cewa lokaci ya yi da ya kamata a shawo kan matsalolin da ke durkusar da fanin ilimi a Najeriya.

A watan Oktoban da ya gabata ne, ASUU ta janye yajin aiki da ta shafe wata takwas tana yi ba tare da ta samu biyan bukatunta daga wajen gwamnatin tarayya ba.

Leave a Reply