Wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga, mai suna Nasanda, ya bukaci gwamnatin jihar Zamfara da ta biya shi kudi Naira miliyan 30 saboda kashe matarsa da kawunta da kuma kanwarta ko kuma ya kashe mutum 300 a matsayin ramuwa.
Rahotanni da dama sun bayyana cewa tuni shugaban ‘yan fashin ya bai wa gwamnatin jihar wa’adin kwanaki 14 na biyan diyyar ta Naira miliyan 30 saboda rashin mutanen uku ko kuma a fuskanci kashe-kashe a jihar.
“Idan gwamnatin jihar ta kasa biyan diyyar, na sha alwashin cewa zan kakkashe al’ummata 300,” inji shi.
A wani faifan sauti da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani, Nasanda ya bayyana kisan da aka yi wa amaryarsa, kawunta da kuma goggonta a matsayin ganganci, inda ya ce ‘yan sakai sun san cewa suna da dangantaka da shi.
A cikin faifan sautin, an ruwaito Nasanda na cewa ya yi adalci kuma ba kwadayi ba ne neman da ya yi na a biya shi diyyar Naira miliyan 30, inda ya kara da cewa da a ce yana da kwadayi, da ya bukaci a ba shi Naira miliyan 50 ga kowane mutum daya daga cikin mutanen da aka kashe.
“Ba zan iya ba da watanni dayawa don gwamnati ta daidaita da ni ba, kwanaki 14 za su isa su biya bukatuna. Kuma ba za mu kai hari ba sai lokacin da mutane suke gonakinsu. Idan ba a bar Fulaninmu su zauna lafiya ba, mu ma ba za mu bar wasu su zauna lafiya ba.
“Idan har gwamnati ba za ta iya biyan Naira miliyan 30 da ake nema ba, ya kamata gwamnati ta shirya don ganin aikin da zan yi. Zan kashe mutum 300 don daukar fansar mutuwar amaryata da ‘yan uwanta biyu. Rayukan 900 za su kasance cikin hadari,” a cewarsa a gargadin kamar yadda VOA ta ruwaito daga Daily Post