BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya isa kasar Amurka a yammacin ranar Alhamis.

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Tiwita, ya je kasar ne domin tattaunawa da jami’an kasar da kuma ‘yan Najeriya mazauna kasar.

“Yanzunan na sauka a birnin Washington D.C domin ganawa da jami’an gwamnati da kuma ‘yan Najeriya mazauna kasar da kuma yan kasuwa.”

Atiku Abubakar ya samu rakiyar Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Bukola  Saraki da Osita Chidoka da sauransu.

Leave a Reply