BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

2023: Mun yi dace da samun Tinubu a APC-Buhari

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce jam’iyyar APC ta yi sa’a da ta samu Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban kasa.

Buhari, wanda shi ne ciyaman na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, ya faɗi haka ne a birnin Landan inda a ke duba lafiyarsa.

A cewar Buhari, Tinubu sanannen ɗan siyasa ne wanda aikin da ya yi a Legas, jihar da ya fi kowacce bunƙasa a Nijeriya, ya cancanci a jinjina masa.

“Damar jam’iyya ta ta cin zaɓe mai ƙarfi ce. Za mu ci zaɓen nan. Dan takarar mu ma shugaban ƙasa, Tinubu sanannen ɗan siyasa ne a ƙasar nan.

“Ya yi gwamna na wa’adi biyu a jihar dsa ta Legas, wacce ta fi ko wacce arziki. Mun yi sa’a da mu ka same shi a matsayin ɗan takara,” in ji Buhari kamad yadda Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.

Leave a Reply