Kano Ayau Hausa, Siyasa

2023: Kwankwaso ne ya fi cancanta -Sheikh Aminuddeen

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Daawah a Kano, Sheikh Muhammad Aminuddeen, ya buƙaci ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso da ya ƙara himma a kan takarar sa ta neman shugabancin ƙasar nan.

Babban limamin, wanda ɗan marigayi shahararren malamin addinin Musuluncin nan ne a Kano, Sheikh Aminuddeen Abubakar, wanda ya kafa ya kafa Gidauniyar Daawah Group of Nigeria kamar yadda muka kalato daga Daily Nigerian Hausa.

Da ya ke gabatar da huɗuba bayan an sallar idi ga dubban masallata da suka hada da Kwankwaso a yau Asabar, limamin ya ce tsohon gwamnan jihar Kano “yana da dukkan kyawawan halaye da zai jagoranci Najeriya kuma ya fi sauran ƴan takarar shugaban kasa na APC da PDP.”

Ya lura cewa MKwankwaso “yana matukar son ci gaban Najeriya”.

Shehin Malamin ya kara da cewa tsohon ministan tsaron abokin mahaifinsa ne, marigayi Sheikh Aminuddeen wanda ya rasu a shekarar 2015.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya kuɓutar da Nijeriya daga kalubalen tsaro da ake fama da shi, Ya kuma yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari jagora ya jagoranci kasar nan cikin nasara.

Sallar ta kuma samu halartar ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a Kano, Abba Kabir Yusuf da abokin takararsa Kwamared Aminu Abdussalam da sauran manyan baƙi.

Leave a Reply