BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Ɗan takarar gwamnan Katsina a APC zai ɗauki Tunde a mataimaki

Dikko Radda, wanda ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Katsina, zai ɗauki ɗa kuma makusanci ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Sabiu Yusuf , wanda a ka fi sani da Tunde, a matsayin nataimakansa a takara, kamar yadda SaharaReporters ta bayyana.

Radda, wanda tsohon Babban Darakta ne na Hukumar Cigaban Kanana da Matsakaitan Masana’antu (SMEDAN), ya taka rawar-gani a zaɓen fidda gwanin takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar, bayan ya doke dukkan mutane uku da ake kyautata zaton za su iya lashe zaɓen.

Ya doke tsohon sakataren gwamnatin Katsina, Dokta Mustapha Inuwa, tsohon Shugaban Kamfanin buga Kuɗi da takardu na Ƙasa, Abbas Umar Masanawa, da kuma tsohon Manajan-Darakta na Bankin Jinginar da Gidaje na Najeriya, Ahmed Dangiwa, a zaɓen na fidda-gwani.

Wata majiya ta shaida wa SaharaReporters cewa wannan matakin da Radda ya dauka, wani salo ne na ya samu kariya, duba da kusancin da Tunde ke da shi da Buhari.

” Shugaban SMEDAN da ya lashe zaben gwamnan jihar Katsina na APC shi ne ya dauki Sabiu Tunde a matsayin mataimakin gwamna ta yadda za a ba shi kariya,” wata majiya ta shaida wa SaharaReporters.

Leave a Reply