Kungiyar ƴan China Masu Kasuwanci ta Najeriya, CBCAN, reshen Jihar Kano, karkashin jagorancin Wakilin Mutanen China, Mike Zhang, ta yi Alla-wadai da kisan Ummulkulthum Buhari (Ummita) da wani dan kasar China, Geng Quanrong ya yi.
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a madadin Wakili ta hannun mataimakinsa Guang Lei, Zhang ya ce ƙungiyar ta yi Alla-wadai da kisan, ta na mai cewa wannan laifi ne da ya kamata hukumomin tsaro da abin ya shafa su kula da shi cikin kwarewa kuma su hukunta wanda ya yi idan har an kama shi da laifi.
A cewar sanarwar, “Al’ummar ƴan China mazauna Kano su na goyon bayan doka da oda yadda ya kamata”.
Har ila yau, al’ummar sun yaba da irin tarba da zama lafiya da aka yi wa ‘yan uwa na kasar Sin mazauna Kano, inda suka yi alkawarin ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda, da sada zumunci da ba da gudummawa ga ci gaban Kano.
Daga nan Mr Zhang ya jajantawa iyalan marigayiyar kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.