BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Zan gyara tsarin tsaron Najeriya-Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce ya zama wajibi ga jami’an tsaron ƙasar su ƙara himma matuƙar ana son a ciyar da ƙsar gaba.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin ganawarsa ta farko da shugabannin hukumomi da rundunonin tsaro na ƙasar a fadarsa da ke Abuja.

A lokacin ganawa da manema labaru, jim kaɗan bayan kammala tattaunawar, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Babagana Monguno ya ce shugaban ya shaida musu cewa ba zai lamunci yanayin da ƙasar za ta rinƙa samun koma-baya ba.

Inda ya ce bai kamata Najeriya ta rinƙa baya-baya ba a lokacin da sauran ƙasashe ke ci gaba.

Ya kuma ce dole ne a samun haɗin kai tsakanin dukkanin ɓangarorin tsaro domin ganin an kawar da duk wata matsalar tsaron da ke addabar ƙasar, kamar yadda muka kalato daga BBC.

A lokacin da ya sha rantsuwa a ranar Litinin, shugaba Tinubu ya sha alwashin magance matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Leave a Reply