Wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa jihohi biyu ne kawai tare da yankin babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja za a iya yin zabukan da ke tafe a Najeriya ba tare da wata matsala ta tsaro ba.
Binciken wanda shugaban Gidauniyar CLEEN Foundation Gad Peter ya gabatar jiya Laraba a Abuja, dangane da nazarin da suka yi kan kalubale ko barazanar da ke tattare da zaben 2023, ya nuna cewa jihohin biyu da Abuja su kadai babu wata fargabar tsaro a tare da su, kamar yadda muka kalato daga BBC.
Peter ya ce jihohi 13 na tattare da babbar barazana ta tsaro yayin da sauran 21 suke da matsalar nan da can.
Ya bayyana sunayen jihohin da ke da matsalar sosai kamar haka, Sokoto, Kebbi, Niger, Benue, Gombe, Bauchi, Plateau, Nasarawa, Taraba, Edo, Delta, Akwa Ibom da kuma Abia.
Shugaban ya ce sun yi wannan nazari ne domin bayar da shawara kan yadda za a bullo wa lamarin domin yin zaben cikin nasara.
Mista Peter ya ce yawan harin da ake kai wa hukumomi da jami’an tsaro da kayayyakin gwamnati da abubuwan jin dadin jama’a abu ne mai tayar da hankali da fargaba.
Ya kara da cewa yanayin hare-haren da ake kai wa cibiyoyi da wuraren tsaro da kayan hukumar zabe alama ce da ke nuna cewa miyagu sun dukufa ganin sun durkusar da kasar ta Najeriya.
Jami’in ya ce Gidauniyar CLEEN ta damu kan irin kalamai na batanci da ake yi da hare-haren da miyagu ke kaiwa kan cibiyoyi da wurare na gwamnati da sauransu, yayin da kasar ke tunkarar zabukan, inda ba a taba samun mutane masu yawa da suka yi rijistar zabe ba a tarihin kasar kamar a wannan lokaci ba.
Gidauniyar ta ankarar da cewa muddin ba a dauki matakan da suka kamata ba, to tana fargabar barazanar za ta iya hana mutane fita su yi zabe, wanda wannan ba karamar asara ba ce, a cewarta.