Hukumar BBC ta sanar da shirinta na rufe gidan rediyon BBC Hausa.
Wannan na zuwa ne a matsayin wani mataki na hukumar na dakatar da shirye-shiryen rediyo da talabijin na Hausa domin komawa kacokam kan yada shirye-shirye ta hanyar intanet.
Ba rediyo da talabijin na Hausa kadai canje-canjen zai shafa ba, har da talabijin na Somalia da Tashar Afrique da sauran tashoshin da ake yada shirye-shirye da yaran Afirka.
Shirye-shiryen radiyo za su koma ta fasahar Podcast, wato rediyon intanet sai kuma sauran fasahohin yada labarai ta intanet.