Majalisar ministoci ta gwamnatin Najeriya ta amince da wata manufa kan amfani da harsunan kasar wajen koyar da dukkan daliban kasar a matakin firamare a fadin kasar.
Ministan Ilimi Adamu Adamu ne ya sanar da haka ga manema labarai, bayan taron majalisar ministoci da aka yi a ranar Laraba cewa majalisar ta amince a aiwatar da sabon tsarin amfani da harsunan gida da ake kira National Language Policy wanda ma’aikatarsa ta kirkiro
Ministan ya bayyana cewa ” ka’idojin koyarwa na shekaru shida na farko a makaruntun firamare za su kasance cikin harshen gida,” kamar yadda muka kalato daga BBC.
Tun kafin Najeriya ta samu ‘yancin-kai daga Birtaniya take amfani da Ingilishi a matsayin harshen hukuma inda cibiyoyin ilimi a kowa ne mataki suke amfani da shi a matsayin harshen gama-gari na koyarwa.
Haka kuma wasu al’ummomi na amfani da harsunan gida tare da Ingilishi a azuzuwa.
A yanzu mahukunta sun ce za a fi ba harsunan gida fifiko a makarantun firamare.
A cewar ministan ilimin Najeriya: ”Yara sun fi koyon abu da sauri, idan aka koyar da su a cikin yarensu na gida.”