A yau Asabar ne za a ba Sabon Sarkin Birtaniya, Sarki Chales sandar mulki.
Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kasance cikin shugabannin kasashen Commonwealth da suka gana da sabon Sarkin na Ingila kafin a fara bikin nadin nasa da za a yi a Fadar Marlborough.
Charles dai ya zama Sarkin Ingila a Satumbar, 2022 bayan da mahaifiyarsa Sarauniyar Ingila Elizabeth ta mutu.
A yau (Asabar) ne dai za a nada shi Sarkin Ingila.